Jami’an kasar Iran sun Jaddada cewa: Suna cikin gagarumin Shirin tunkarar duk wata barazana amma ba su son fara kunna watar yaƙi a yankin
Babban Hafsan Hafsoshin Sojojin Iran, Manjo Janar Abdulrahim Mousavi, da Kwamandan Sojojin Iran, Manjo Janar Amir Hatami, sun tabbatar da cewa: Iran ba ta neman fara yaki a yankin duk da cikakken shirinta. Sun yi gargadin cewa: Duk wani tashin hankali zai kawo cikas ga zaman lafiyar yankin tsawon shekaru, yayin da a lokaci guda suka jaddada cewa sojojin suna sa ido sosai kan abokan gaba kuma suna shirye su mayar da martani mai kyau ga duk wata barazana.
A wani taro da aka yi a jiya Lahadi, tare da gungun kwamandoji da ma’aikata daga Sojojin Sama da Sojojin Tsaron Sama, Manjo Janar Mousavi ya ce: “Duk da shirye-shiryen Iran, da gaske ba ta son fara yakin yankin. Duk da cewa masu fara kai harin wuce gona da iri su ne ke tayar da rikicin yakin yankin, barkewarsa ba shakka za ta jinkirta ci gaba da habakan yankin tsawon shekaru da yawa, kuma mummunan sakamakonsa zai fada kan masu kai hari, wato Amurka da yahudawan Sahayoniyya.”
Manjo Janar Mousavi ya kara da cewa: “Bayan tsaro mai tsarki, wasu yake-yaken sun kuno kai, ciki da yakin kakaba takunkumai, yakin neman killace Iran. Amma ba a kayar manufofin Iran ba, maimaikon haka Iran ta fara samun karfin dogaro da kai, da haɓakan ilimin gida, kuma Rundunar Sojan Sama ta zama rundunar da ta dogara da ilimi, wanda hakan ya tabbatar da cewa ƙarfi ba ya dogara da wasu; maimakon haka, dogaro da wasu yana haifar da rauni.