Jami’an tsaron Falasdinawa sun kashe wani Bafalasdine da dansa a sansanin ‘yan gudun hijira da ke birnin Jenin a Gabar Yammacin Kogin Jordan
Rahotonni sun bayyana cewa: Jami’an tsaron hukumar Falasdinu sun kashe wani bafalasdine da dansa, tare da raunata ‘yarsa sosai, a lokacin da suke kan rufin gidansu da ke sansanin ‘yan gudun hijira na sansanin Jenin, lamarin da ya Sanya adadin Falasdinawa da suka yi shahada sakamakon hare-haren jami’an tsaron hukumar cin gwarya-kwaryar gashin kan Falasdinawa tun bayan fara samame kan yankin a kasa da wata guda suka kai Falasdinawa takwas.
Majiyoyin cikin gida sun tabbatar da mutuwar magidanci mai suna Muhammad al-Hajj (dan shekaru 43 a duniya) da yaronsa, Qasim Mahmoud al-Hajj mai shekaru 14, yayin da diyar shahidin ta samu munanan raunuka, bayan da jami’an tsaron hukumar Falasdinawa suka bude musu wuta, yayin da suke kan rufin gidansu da ke kusa da kofar shiga sansanin Jenin ta gabas da ake kira kofar jiwar dawaki.
Majiyar ta bayyana cewa mahaifin da dansa nan take suka yi shahada kuma an kai diyar shahidin zuwa asibiti tare da munanan raunuka.