Babban hafsan hafsoshin sojan kasar Iran Manjo Janar Sayyid Abdurrahim Musawi ya ce, duk wani kurskure da abokan gaba za su yi zai haddasa yaki ne a fadin wannan yankin na yammacin Asiya da hakan zai jefa Amurka da dukkanin kawayenta a cikin hatsari na tsaro.
Kamfanin Dillancin Labarun “Mehr” na Iran ya ambato cewa: Manjo Janar Musawi ya yi wannan bayanin ne a lokacin da yake duba zaman Shirin da sojojin kasar ta Iran suke ciki domin fuskantar abokan gaba.
Da yake Magana akan yadda Iran ta dade tana fuskantar kiyayya daga Amurka, Manjo Janar Musawi ya kara da cewa; A kodayaushe Iran tana jajurcewa a gaban siyasar nuna girman kai da hakan yake tilasta wa makiya ja da baya.
Haka nan kuma babban hafsan hafsoshin sojan kasar ta Iran ya yi Ishara da yakin bayan nan da abokan gabar su ka shelanta akan Iran, mai fuskoki da dama, da ayyukan ta’addanci, sai dai kuma Iran ta rusa lissafin makiyan.
Manjo Janar Musawi ya kuma ce, A cikin shekaru 47 na juyin musulunci, Iran ta tabbatar da cewa ba kasa ce da za a iya hadiye wa ba,don haka abokan gabar da basu iya daukar darasi a baya ba, za su sake cin kasa.
Haka nan ya yi Ishara da kallafaffen yakin Iraqi akan Iran da kuma yakin bayan nan na kwanaki 12, sai kuma ayyukan ta’addanci na kusa-kusan nan a watan Janairu, sannan ya ce; Iran ta yi nasarar dakile dukkanin makarkashiya da makircin Amurka da Isra’ila.
Akan batun yiyuwar killace Iran ta ruwa, Manjo Janar Musawi ya ce; bagiren da kasar take cikinsa zai sa hakan ba zai taba faruwa ba.