Sakonni suna ci gaba fitowa daga Iran a matakai daban-daban musamman daga manyan jami’ai, inda suke jaddada wajabcin mayar da martani ga kisan gillar da haramtacciyar kasar Isra’ila ta yi wa shahidi Isma’il Haniyah a matsayin lamari da babu makawa, kuma babu ja da baya ciki, wanda a baya bayan nan da ya jaddada wajabcin mayar da martanin shi ne mataimakin kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran Birgediya Janar Fadavi.
Mataimakin kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na kasar Iran Birgediya Janar Ali Fadavi ya jaddada cewa: Umurnin Jagoran juyin juya halin Musulunci a bayyane yake a fili dangane da azabtar da yahudawan sahayoniyya ‘yan mamayar da kuma daukar fansar jinin shahidi Isma’il Haniyah.
A tattaunawarsa da gidan talabijin na Al-Mayadeen, Fadavi ya jaddada cewa: Dole za a aiwatar da umarnin jagoran juyin juya halin Musulunci ta hanyar da ta dace, kuma wannan shi ne aikin Iran ta sanya a gaba a halin yanzu.
Mataimakin kwamandan dakarun kare juyin juya halin ya kuma yi la’akari da cewa: Zaben Yahya Sinwar a matsayin madadin shahidi Isma’il Haniyah yana nufin cewa hanyar gwagwarmaya da kungiyar Hamas ta fara zata ci gaba har zuwa karshe.