Yan a ware na jihar Alberta ta kasar Canada, wanda kuma suke kokarin ballewa daga kasar ta Canada saboda dimbin arzikin man fetur wanda yankin yake da shi, sun sha ganawa da Jami’an gwamnatin Trump don samun taimakon sa.
Jaridar The Nation ta kasar Amurka ta bayyana cewa taro na karshen da bangarorin biyu suka gudanar an yi shi ne a asirce a cikin fasalan ruwan sama a shekarar da ta gabata. Wannan halin na shugaba Trump ya fusata firay ministan kasar Canada Mark Carney, wanda ya fara daukar matakin kauracewa Amurka, inda yake kara karfafa harkokin kasuwanci da siyasa masu karfi da kasar China. Ba’a dade ba Carney ya ziyarci kasar China. Wannan ma wani hatsarin ga Amurka nan gaba.