Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya bayyana cewa; Barazana ga cibiyoyin nukiliyar Iran keta yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya ce
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i, yayin da yake mayar da martani ga kalaman kiyayya da mai baiwa Amurka shawara kan harkokin tsaro Jake Sullivan ya yi, ya bayyana cewa: An sha maimaita wannan batu, duba da cewa, ta fuskar shari’a, barazana yin amfani da karfi tuwo kan cibiyar nukiliyar wata kasa, cin zarafi ne ga yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya.
A safiyar yau Litinin ne kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran a taron manema labarai ya yabawa irin rawar da kuma sadaukarwar shahidi kwamanda Qassim Suleimani, wanda ake yi wa kallon jarumin yaki da ta’addanci, yana mai nuni da cewa a gobe 7 ga watan Janairu ne ranar shahidai a Falastinu, don haka ya bayyana cewa: A kan wannan lokaci dole ne a ambaci laifukan da ke gudana da aiwatar da kisan kiyashi da suke manyan abubuwan kunya da gwamnatin yahudawan sahayoniyya da masu goya musu baya suke aikatrawa.
Baqa’i ya ci gaba da cewa: A cikin ‘yan kwanakin nan, Falasdinawa da dama da ba su ji ba ba su gani ba, da suka hada da mata, yara da marasa lafiya, sun yi shahada a yankuna daban-daban na Zirin Gaza, inda ya kara da cewa tsananin sanyin da ake fama da shi a kwanakin nan ya ba da wani sabon salo ga wannan lamari mai cike da bakin ciki, kuma abubuwan da suke faruwa a Zirin Gaza suna tuna mana wata waka da mawakin Falasdinu Mahmoud Darwish ya rubuta inda ke cewa: “Idan suka tambaye ka game da Gaza, ka ce musu akwai shahidi, shahidi zai taimake shi, shahidi zai dauki hotonsa, wani shahidin ya yi bankwana da shi, sannan kuma shahidi yana masa addu’a”.