Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Iran ba ta taba shirin kashe Donald Trump ba
Shugaban kasar Iran, Masoud Pezeshkian, ya yi watsi da zargin da yahudawan sahayoniyya da wasu kasashe sukeyi game da yunkurin Iran na kashe zababben shugaban Amurka Donald Trump.
A wata hira da ya yi da tashar talabijin ta NBC ta Amurka, shugaba Pezeshkian ya mayar da martani ga wata tambaya cewa: “Daya daga cikin abubuwan da ke iya barazana ga harkokin diflomasiyya na iya zama cewa Amurka ta yi imanin cewa Iran na da wani shiri na kashe Donald Trump?” Shugaba Pezeshkian ya amsa da tambayar cewa: “Dukkan kashe-kashen da ake gani a yankin da Turai da sauran wurare, ko an taba samun hannun Iran a cikinsu?”
Da yake mayar da martani ga wasu tambayoyin cewa: “Shin Iran ba ta taba wani shirin kashe Trump ba? “Shin Iran ta yi alkawarin ba za ta dauki wani mataki na kashe Donald Trump ba?” Shugaba Pezeshkian ya mayar da martini da cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba ta dauke da irin wannan niyya tun daga farko kuma ba zata kudurta wannan niyyar ba.