Ministan harkokin wajen kasar Chadi ya sanar da soke yarjejeniyar hadin gwiwa ta tsaro da kasar Faransa
Rahotonni daga Chadi sun bayyana cewa: Jamhuriyar Chadi ta sanar da soke yarjejeniyar hadin gwiwa ta tsaro da kasar Faransa.
Ministan harkokin wajen kasar Chadi Abdur-Rahmane Kalamullah a ranar Alhamis da ta gabata ya sanar da cewa: Kasarsa ta soke yarjejeniyar hadin gwiwa ta tsaro da Faransa, sa’o’i kadan bayan ziyarar takwaran aikinsa na Faransa Jean-Noel Barrot a birnin N’Djamena fadar mulkin kasar ta Chadi.
Kalamullah a cikin wata sanarwa da ma’aikatarsa ta wallafa a shafinta na Facebook, ya ce: Gwamnatin Jamhuriyar Chadi tana sanar da al’ummar Chadi da na kasa da kasa game da matakin da ta dauka na soke yarjejeniyar hadin gwiwar tsaro da aka kulla tsakaninta da Jamhuriyar Faransa.