Ma’aikatar harkokin wajen jamhuriyar Azerbaijan ta fitar da wani bayani da a ciki ta ce, ba za ta taba barin ayi amfani da iyakokinta domin kawo wa makwabciyarta Iran harin soja ba.
Kamfanin dillancin labarun “Anatoli” na Turkiya ya nakalto bayanin da ma’aikatar harkokin wajen ta jamhuriyar Azerbaijan ta fitar bayan tattaunawa ta wayar tarho da aka yi a tsakanin ministan wannan ma’aikata Jaihun Bairamov da takwaransa na Iran Abbas Arakci.
Ministan harkokin wajen na Azerbaijan ya nuna matukar damuwa akan halin dar-dar da ake ciki a wannan yanki, kuma kasar tana yin kira ga dukkanin bangarori da su kaucewa amfani da maganganun da za su jawo rikici.
Har ila yau ministan harkokin wajen na jamhuriyar Azerbaijan ya kuma yi kira da a bude tattaunawa domin warware sabanin da ake da shi da aiki da dokokin kasa da kasa.