Jakadan Rasha A M D D Yayi Watsi Da Daukar Matakin Soja Kan Kasar Iran

jakadan kasar rasha a majalisar dinkin Duniya yayi watsi da duk wani shiri na daukar matakin soji kan kasar iran kuma yayi gargadin cewa matakin

jakadan kasar rasha a majalisar dinkin Duniya yayi watsi da duk wani shiri na daukar matakin soji kan kasar iran kuma yayi gargadin cewa matakin zai iya wargaza zama lafiya a fadin yankin baki daya, don  haka Moskon a shirye take ta goyi  bayan matakin diplomasiya ba tare da sai an sanyata a matsayin mai shiga tsakani ba.

Jakadan din din na kasar Rasha a majalisar dinkin duniya Vasily Nebenzy a yau Alhamis ya jaddada cewa yin amfani da karfin soji kan iran da kasashen turai musamman ma Amurka ke kokarin yi to zai fuskanci mummunan sakamako, kuma ya zama wajibi a guji afkuwar haka.

haka zalika da yake tattaunawa da manema labarai yace muna fatan cewa Amurka da sauran kawayenta za su yi  amfani da hikima domin ba za’a taba amincewa da duk wani mataki na soji ba domin yana da hadari sosai kuma zai iya haifar da sakamako mara dadi a yankin.

ana sa ran ministan harkokin wajen kasar iran zai jagoranci tawagar kasar wajen tattaunawar da ya hada da Majid takht Ravanchi da Kazem Gharib abadi, yayin da ita kuma Amurka Steve Witkof zai wakilci fadar white hause a wajen zaman.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted