Jakadan Nijar A Iran, Ya Mika Takardar Kama Aikinsa Ga Shugaba Pezeshkian

Jakadan Jamhuriyar Nijar a Iran, Seydou Zataou Ali, ya mika takardar kama aikinsa ga shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian a wannan Litini 30 ga watan

Jakadan Jamhuriyar Nijar a Iran, Seydou Zataou Ali, ya mika takardar kama aikinsa ga shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian a wannan Litini 30 ga watan Satumba 2024.

A al’adar diflomasiyya, gabatar da wasikun amincewa ga shugaban kasar da ke karbar jakada na nufin amincewa da shi da kuma soma aikinsa gadan-gadan.

A yayin ganawar bangarorin sun tattauna hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu da kuma hanyoyin karfafa su.

Jami’in diflomasiyyar na Nijar ya yaba da kyakkyawar alakar sada zumunci da hadin gwiwa tsakanin Nijar da Iran, kasashe biyu mambobi na Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar hadin kan musulmi da ke da akidar samar da zaman lafiya, hadin kai, ‘yan uwantaka da mutunta hurumin kowace kasa.

Jakadan ya tabo yanayin siyasar Nijar da ke da nasaba da zuwan Majalisar Ceton Kasa ta (CNSP) da jarumtakar gwagwarmayar da al’ummar Nijar suka yi na kwato ‘yancinsu da martabarsu.

Ya kuma yi tsokaci kan hangen nesa na shugaban kasar Birgediya Janar Abdourahamane Tiani, da nufin mayar da Nijar ta zama kasa mai tasowa wanda ke sa a ji muryarta a fagen kasa da kasa.

Daga nan sai ya gode wa gwamnatin Iran bisa dukkan shirye-shiryen da aka yi domin fara gudanar da ayyukan tawagarsa cikin inganci.

A nasa bangare Shugaban kasar ta Iran ya yaba da kyakyawar alakar da ke tsakanin Nijar da Iran tare da fatan bude wani sabon shafi na hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu.

Ya yi maraba da irin ci gaban da al’ummar Nijar ke samu a halin yanzu na ‘yantar da su a fagen siyasa da tattalin arziki da al’adu da kuma burin gwamnati na samar da sabbin abokan hulda.

Daga karshe shugaba Pezeshkian na Iran ya baiwa jakadan na Nijar tabbacin bada goyon bayan sa wajen samun nasarar aikinsa a Iran.

A watan Agustan da ya gabata ne ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran na riko, Ali Bagheri Kani ya karbi kwafin wasikun fara aiki na sabon jakadan Jamhuriyar Nijar a kasar.

kasasahen Nijar da Iran dai sun jaddada aniyarsu ta ci gaba da karfafa huldar hadin gwiwa a fannoni daban daban.

A tare sun yi alkawarin yin aiki don karfafawa da daidaita dangantakarsu, musamman yarjejeniyoyin da kasashen biyu suka rattaba hannu a kai a ziyarar da firaministan Nijar, Mohamed Lamine Zein ya kai a watan Janairun 2024 a Tehran, inda aka rattaba hannu kan yarjeniyoyi da dama a fannonin makamashi, kiwon lafiya masana’antu da al’adu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments