Jagoran Adawa Ya Lashe Zaben Shugabancin Yankin Somaliland

Rahotanni sun bayyana cewa, an zabi Abdirahman Mohamed Abdullahi, shugaban ‘yan adawar Somaliland a matsayin shugaban yankin Somaliya mai ballewa. Abdullahi – wanda aka fi

Rahotanni sun bayyana cewa, an zabi Abdirahman Mohamed Abdullahi, shugaban ‘yan adawar Somaliland a matsayin shugaban yankin Somaliya mai ballewa.

Abdullahi – wanda aka fi sani da Cirro – na jam’iyyar Waddani – ya samu kusan kashi 64 na kuri’un da aka kada, inda ya doke shugaba mai ci, Muse Bihi Abdi na jam’iyyar Kulmiye, in ji hukumar zabe ta Somaliland (NEC) a ranar Talata, kamar yadda kafafen yada labarai na cikin gida suka ruwaito. Kamfanin dillancin labaran Associated Press.

Masu kada kuri’a a yankin Somaliya da ke ballewa sun kada kuri’a a makon da ya gabata a zaben da aka shafe tsawon shekaru biyu ana yi saboda rashin kudi da wasu dalilai.

Abdi, wanda ke neman wa’adi na biyu bayan shafe shekaru bakwai yana mulki, ya samu kashi 35 cikin dari na kuri’un da aka kada.

Dukkan ‘yan takarar sun yi yakin neman zabe tare da yin alkawarin farfado da tattalin arzikin da ke cikin mawuyacin hali tare da ingiza kokarin samun karbuwa a duniya ga Somaliland.

Somaliland, wacce ta ayyana ‘yancin kai a shekarar 1991, yayin da Somaliya ta fada cikin rikici, ta gina ingantaccen yanayi na siyasa, sabanin yadda Somaliya ke fama da matsalar tsaro.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments