Jagora: “Yan Sahayoniya Su Saurari Ukuba Mai Tsanani

Jagoran juyin juya halin musulinci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya fitar da bayani a yau juma’a da a ciki ya yi wa ‘yan

Jagoran juyin juya halin musulinci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya fitar da bayani a yau juma’a da a ciki ya yi wa ‘yan sahayoniya alkawalin fuskantar ukuba mai tsanani.

Bayanin na jagora ya kunshi cewa:

Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai

Ya Ku Al’ummar Iran Masu Girma

Da safiyar yau, ‘yan sahayoniya sun miko hannuwansu da suke jike da jini, domin tafka laifuka a cikin kasarmu.  Sun kuma sake bayyana hakikanin dabi’arsu mummuna fiye da kowane lokaci a baya,  su ka kai wa  gidajen fararen hula hari. A dalilin haka, wannan haramtacciyar kasar ta saurari sakamako mai tsanani.

Su kuma  sani cewa; Sojojin Jamhuriyar musulunci masu karfi ba za su kyale su ba da yardar Allah. A yayin wannan harin kwamandoji da dama da masana sun yi shahada.

Wannan laifin da ‘yan sahayoniya su ka tafka, ya sa sun shirya wa kansu makoma mai tsanani da daci, za su kuma ga hakan babu tantanma.

Sayyid Ali Khamnei

13/06/2025

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted