Ayatullah Khamenei ya gana da firaministan Pakistan Shehbaz Sharif. Jagoran ya nuna matukar godiya ga yadda gwamnati da kuma ‘yan uwantaka na Pakistan suka nuna mata.
Ya ce Iran na ba da fifiko kan dangantakarta da Pakistan, kuma ta yi imani da yuwuwar inganta dangantakar a karkashin sabuwar gwamnatin Pakistan.
Jagoran ya kara da cewa, “Ba kullum huldar abokantaka ke tafiya ba tare da fskantar cikas ba, don haka dole ne mu shawo kan cikas, mu ci gaba da samun ci gaban hadin gwiwa cikin azama da kuma a aikace.”