Search
Close this search box.

Jagora : Tun Kafin Zamanin Imam Hussein Ake Yaki Da Zalunci

Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya ce tun kafin zamanin Imam Husaini (AS) ana ci gaba da yaki da zalunci, inda

Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya ce tun kafin zamanin Imam Husaini (AS) ana ci gaba da yaki da zalunci, inda ya kara da cewa yakin ya dauki salo daban-daban a lokuta daban-daban.

Jagoran ya bayyana hakan ne yau Lahadi yayin juyayin kwanaki Arba’in, bayan shahadar Imam Husaini (AS), limamin Shi’a na uku.

Ayatullah Khamenei ya ce ana ci gaba da gwabzawa tsakanin bangaren Husaini da ke yaki da zalunci da kuma azalumai da zalunci.

Jagoran ya kuma bayyana cewa, wadannan bangarori guda biyu sun wanzu tun kafin zamanin Imam Hussien (AS) har zuwa yau kuma haka za ta kasance.

Kuma Wannan yakin yana da siffofi daban-daban, inji shi.

Share

1 1 vote
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments