Jagora: Tabbas Samarin Syria Za Su Kawar Da Sansanonin Amurka Dake Cikin Kasarsu

Jagoran juyin juya halin musulunci na Iran Ayatullah sayyid Ali Khamnei wanda ya gabatar da jawabi da safiyar yau Laraba ya ce; Tabbas samarin kasar

Jagoran juyin juya halin musulunci na Iran Ayatullah sayyid Ali Khamnei wanda ya gabatar da jawabi da safiyar yau Laraba ya ce; Tabbas samarin kasar Syria za su take sansanonin Amurka da kafafunsu, kuma za su sami nasara da murkushe wadanda su ka mamaye kasarsu, ko badade ko bajima.

Jagoran juyin juya halin musuluncin na Iran Sayyid Ali Khamnei ya kuma ce; Duk wata kasa wacce ta janye sanadarorinta na karfi da take da su, to abinda ya faru da Syria  na mamayar Amruka da HKI da wasu kasashen yanki, zai iya faruwa da ita.”

Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya kuma kara da cewa; Duk wanda ya kutsa cikin Syria, samarin Syria  ‘yan gwgawarmaya za su tilasta masa janyewa.”

 Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya kuma bayyana cewa fagen dagar dake kare gaskiya zai yi nasara babu shakka, tare da yin ishara da yadda masu kare Harami, su ka sami nasarori a cikin shekarun bayan nan da hakan yake tabbatar da cewa juyin musulunci yana a raye.

Bugu da kari jagoran juyin musuluncin na Iran ya yabawa fagagen dagar Lebanon da Yemen, tare da bayyana su a matsayin wasu alamomi na gwagwarmaya da  za su zami nasara.

Jawabin jagroan joyin musuluncin na Iran dai ya zo ne a daidai lokacin da ake tunanawa da zagayowar lokacin shahadar Shahid Kassim Sulaimani wanda ya kasance gwarzon kafa fagagen daga na gwagwarmaya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments