Jagoran Juyin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya bayyana cewa, ko kadan kasar ba za ta yi sassauci wajen fuskantar mabarnata ba.
Jagoran ya bayyana hakane ne a wani jawabinsa jiya Juma’a a yayin karbar bakuncin dubban mutanen da suka kawo masa ziyara daga birnin Qum.
“Ya kamata kowa ya san cewa jamhuriyar musulunci ta Iran an kafa ta ne ta hanyar sadaukar da kan dubun dubatar mutane masu niyya mai kyau da daukaka, don haka ko kadan ba za ta yi sassauci wajen fuskantar masu barna ba.”
Jagoran juyin musuluncin na Iran ya yi Ishara da kone-konen da wasu tsirarun mutane su ka yi a daren Juma’a a sassa daban daban na Iran tare da barnata gine-ginen kasarsu saboda kawai su farantawa shugaban kasar Amurka rai.
Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya kuma ce, shugaban kasar Amurka wanda hannuwansa suke jike da jinin fiye da mutanen Iran 1,000 da kuma kwamandoji da masana fasahar Nukiliya da su ka yi shahada a lokacin yakin kwanaki 12, ya yi furuci da cewa shi ne da kansa ya jagoranci yaki, amma yanzu ya fito yana cewa, yana goyon bayan al’ummar Iran, sannan kuma sai a sami wasu mutane da ba su san abinda yake faruwa su fito suna yin kone-kone.
Jagoran juyin musuluncin na Iran ya ci gaba da cewa, to ya kamata kowa da kowa ya sani cewa ta hanyar sadaukarwar duban mutane aka kafa wannan jamhuriyar musuluncin don haka babu maganar yi wa masu barna sassauci. Haka nan kuma ya ce jamhuriyar musulunci ba za ta lamumta da duk wani dan kore ba.
Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya kuma ce; Da izinin Allah jamhuriyar musulunci za ta ci gaba da bunkasa kowace rana, kuma makircin makiya zai ci kasa.