Jagoran juyin juya halin musulinci na Iran,Ayatullah Sayyid Ali Khamenei, ya bayyana cewa yau duniyar musulmi tana bukatar hadin kai fiye da ko wane lokaci.
A yayin ganawarsa da jami’an tsare-tsare da jakadun kasashen musulmi yau Litinin ranar karamar sallah a Iran, Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran ya mayar da hankali kan abubuwan da ke faruwa a yankin inda ya ce a yau wani bangare na duniyar musulmi ya samu munanan rauni.
‘’ Falasdinu ta ji rauni, Lebanon ma ta ji rauni, inji shi. Laifukan da aka aikata a wannan yanki ba a taba ganin irinsa ba, an kashe yara kusan 20,000.”
Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bukaci a hankali tare da daukar nauyin da ya rataya a kan wannan lamari.
“A yau, hakika duniyar musulmi tana bukatar hadin kai inji jagoran.