Jagora : A yau, duniyar musulmi tana bukatar hadin kai

Jagoran juyin juya halin musulinci na Iran,Ayatullah Sayyid Ali Khamenei, ya bayyana cewa yau duniyar musulmi tana bukatar hadin kai fiye da ko wane lokaci. A yayin ganawarsa da jami’an tsare-tsare da jakadun kasashen musulmi yau Litinin ranar karamar sallah a Iran, Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran ya mayar da hankali kan abubuwan […]

Iran ta gargadi Amurka kan barazanar harin bam da Trump ya yi

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta gayyaci mai kula da harkokin kasar Switzerland da ke Tehran domin nuna fishi kan irin munanan ayyukan Isra’ila a yankin da kuma barazanar da shugaban Amurka Donald Trump ke yi kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran. Babban daraktan ma’aikatar harkokin wajen Iran Issa Kameli ne ya gayyaci jami’in diflomasiyyar na […]

Gaza : Fiye da mutane 1,000 Isra’ila ta kashe tun daga ranar 18 ga Maris

A Gaza fiye da mutane 1,000 ne Isra’ila ta kashe tun daga ranar 18 ga watan Maris, tun bayan sake dawo da yaki a Zirin. Hakan ya sanya adadin falasdinawan da Isra’ila ta kashe tun watan Oktoba ya kai 50,350 tare da raunata 114,400 a cewar ma’aikatar lafiya ta Gaza. Hare-haren da Isra’ila ta kai […]

Faransa : An haramta wa Marie Le Pen, takara har tsawon shekaru 5

A Faransa, an haramta wa Marie Le Pen yin takara har na tsawon shekaru biyar kuma hakan na nufin ba za ta yi takarar shugabancin kasar ba a shekarar 2027. An dai samu yar siyasar ne da laifin almubazzaranci da kudaden jama’a wajen daukar nauyin jam’iyyarta ta National Rally mai tsaurin ra’ayi.   An tuhumi […]

An Fara Yakin Neman Zabe A Kasar Gabon

Jam’iyyun siyasa a kasar Gabon sun fara yakin neman zabe wanda za’a gudanar a ranar 12 ga watan Afrilu na wannan shekara ta 2025 a jiya Asabar. Kamfanin dillancin labaran Sputnik na kasar Rasha ya nakalto shugaban kasar Riko Brice Clotaire Oligui Nguema wanda ya jagoranci juyin mulki wa tsohon shugaban kasar Ali Bongo, sannan […]

Iran Ta Zama Zakara A Wasan Kwallon Kafa Ta Bakin Teku Karo Na 4 Asiya

Yan wasan kwallon kafa na kasar Iran sun zama zakara karo na 4 a kwallon kafa na yashin bakin teku a karo na 4 a cikin kasashen Asiya. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ba bayyana a gasa ta karshe wanda kungiyar kwallon kafa ta yashin bakin take wanda aka gudanar tsakanin JMI da […]

Jiragen Yakin Amurka Sun Kai Sabbin Hare-Hare Kan Kasar Yemen A Daren Jiya

Jiragen yakin Amurka sun kai sabbin hare-hare kan kasar Yemen a daren Lahadi a wasu yankuna a birnin San’aa babban birnin kasar. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bada sanarwan cewa a safiyar yau Litinin ne jiragen yakin Amurkan suka kai hare-hare har  13 a kan wurare daban-daban a kasar, daga ciki har […]