Shugaban kasar Cote d’Ivoire, Alassane Ouattara ya sanar da cewa bisa manufar sake tsara sojojin Faransa a nahiyar Afirka, a watan Janairun nan za a karbi sansanin sojin Faransa da ke Abidjan.
Alassane Ouattara ya jaddada cewa “Za mu iya yin alfahari da sojojin mu, wadanda zamanintar su ta yi tasiri a yanzu.
“A cikin wannan yanayi ne kuma muka yanke shawarar shirin ficewar sojojin faransa daga Cote d’Ivoire a tsarin hadin gwiwa,” in ji shugaban na Ivory Coast a jawabinsa na sabuwar shekara.
Don haka, sansanin na BIMA na 43, bataliyar sojojin ruwa na Port-Bouet, za a mayar da su ga sojojin Cote d’Ivoire daga wannan wata na Janairu 2025, “in ji shi.
Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar da rahoton cewa, za a sanya wa sansanin sunan Janar Ouattara Thomas Aquinas, babban hafsan hafsoshin sojin Ivory Coast na farko.
Faransa ta yanke shawarar sake fasalin sojojinta a Afirka, bayan korar ta daga kasashen Sahel uku da ke karkashin mulkin sojan da ke adawa da Paris.
Ivory Coast ta kasance muhimmiyar aminiyar Faransa a yammacin Afirka, tana da sojoji kusan 1,000 a bataliyar BIMA ta 43, bisa ikirarin da ta ke na taimakawa a yakin da ake yi da masu ikirari da sunan jihadi da ke kai hare-hare a yankin Sahel da arewacin wasu kasashe a mashigin tekun Guinea.