Sojojin Isra’ila sun kashe ‘yan jarida biyar Falasdinawa a wurare daban-daban a Zirin Gaza a cikin kwana guda, kamar yadda ofishin watsa labarai na gwamnatin Gaza ya tabbatar a ranar Asabar.
A wata sanarwa da ofishin ya fitar, adadin ‘yan jaridar da Isra’ila ta kashe tun bayan soma yaƙin ya zama 158.
Ofishin yada labarai na gwamnati da kungiyoyin kare hakkin bil adama sun yi gargadi sau da dama kan cewa sojojin Isra’ila suna kai hare-hare kan ‘yan jaridar Falasdinawa da gangan tun farkon yakin Gaza don hana ba da rahoton “laifi” a yankin.
Hare-haren jiragen Isra’ila maras matuƙa sun faɗa kan wurare da dama a Birnin Gaza da sansanonin gudun hijira na Maghazi da Nuseirat inda suka yi sanadin mutuwar aƙalla farar hula 11 da kuma jikkata wasu da dama, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na WAFA ya sanar.
Waɗanda suka shaida lamarin sun bayyana cewa mutum tara ne suka mutu a lokacin da sojojin na Isra’ila suka kai hari a wani gida da kuma wurin ajiye kayayyaki na hukumar UNRWA a Maghazi da Nuseirat.
Haka kuma majiyoyi sun tabbatar da kashe farar hula biyu a harin da Isra’ila ta kai kan wani gini a cikin Birnin Gaza.