Da safiyar yau Juma’a jirgin sama maras matuki na Haramtacciyar Kasar Isra’ila ya kai hari a yankin al-Shalihat a kusa da garin Khayyam a kudancin Lebanon.
Bugu da kari, tankokin yakin na Haramtacciyar Kasar Isra’ila tare da wasu motocin soja sun kutsa cikin garin Yarun, inda su ka tsaya a bakin wani gida wanda a baya su ka tarwatsa shi.
Sai dai bayan wani lokaci kadan, sojojin Lebanon tare da na rundunar MDD ta tabbatar da zaman lafiya “UNIFIL” sun isa zuwa yankin da jiragen saman na yan sahayoniya su ka kai wa harin.
Dama dai tun da marecen jiya Alhamis ne dai sojojin na ‘yan sahayoniya su ka kai wasu hare-hare da manyan bndigogi akan garin Yarun, haka nan kuma sun kai wani harin a garin Biyadh Balida.