Masu shiga tsakani daga Amurka, Turai da ƙasashen Larabawa sun ƙara ƙaimi wajen ganin an kauce wa shiga gagarumin yaƙi tsakanin Isra’ila da mayaƙan Hezbollah na ƙasar Lebanon waɗanda ke samun goyon bayan Iran, suna masu fargabar watsuwarsa zuwa sauran sassan Gabas ta Tsakiya kamar yadda aka yi hasashe watanni da dama da suka wuce.
Iran ta gargadi Isra’ila danane da yuwuwar barkewar wani sabon yaki , matukar dai gwamnatin yahudawan ta yi gigin kaddamar da farmaki kan kasar Lebanon da sunan yaki da Hizbullah.
Yanzu dai babu tabbas game da tsagaita wuta a yaƙin da Isra’ila take yi a Gaza, wanda hakan ne kawai zai sa Hezbollah da sauran ƙungiyoyi gwagwarmaya su sauƙaƙa shirinsu na gwabza yaƙi da Isra’ila.
Ganin cewa babu ci gaba a tattaunawar tsagaita wuta, jami’an diflomasiyya na Amurka da sauran ƙawayenta sun gargaɗi Hezbollah game da far wa Isra’ila da yaƙi.