A daidai lokacin da yakin Gaza yake cika kwanaki 428 HKI tana cigaba da tafka kisan kiyashi akan al’ummar Falasdinu.
Majiyar asibiti ta fada wa manema labaru cewa HKI ta kai wasu hare-hare a arewacin Gaza a jiya Juma’a wanda ya yi sanadin shahadar Falasdinawa 63 da kuma jikkatar wasu 35.
Bugu da kari yankin na Arewacin Gaza yana fuskantar matsananciyar yunwa saboda yadda HKI ta hana shigar da duk wani kayan agaji saboda tilastawa Falasdinawa su yi hijira.
Kafafen watsa labarun HKI sun ambato wata majiyar gwamnatin Amurka tana cewa,an kusa dage takukumin hana shigar da kayan agaji zuwa yankin Arewacin Gaza.
Kwanaki kadan da su ka gabata hukumar Agaji ta MDD a Falasdinu “Unrwa’ ta sanar da matsanancin halin da mutanen Gaza, musamman a arewacinsa suke ciki, saboda rashin abinci da magani.
Hukumar ta bayyana yadda a cikin shekara daya ta gabatar da bukatu masu yawa na a bar ta ta shigar da kayan agaji zuwa yankin amma ba a amince da mafi yawancinsu ba.
Amfani da yunwa a mastayin makamin yaki yana daya daga cikin laifukan da ka tuhumi gwamnatin Natenyahu da aikatawa a kotun duniya ta manyan laifuka.