Isra’ila ta yi barazanar kashe al-Houthi na Yemen saboda goyan Falasdinu

Gwamnatin Isra’ila ta yi barazanar kashe jagoran kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen, Abdul-Malik al-Houthi, idan har Sana’a ta ci gaba da kai hare-hare da makami

Gwamnatin Isra’ila ta yi barazanar kashe jagoran kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen, Abdul-Malik al-Houthi, idan har Sana’a ta ci gaba da kai hare-hare da makami mai linzami kan Isra’ilar don goyon bayan Falasdinu.

Ministan harkokin soji na gwamnatin, Isra’ila Katz ya ce idan har Yemen ta ci gaba da ayyukanta “za su sha azaba mai radadi.” 

Katz ya ce kisan da gwamnatin za ta wa al-Houthi zai yi kama da kisan gilla kan “Deif da Sinwars a Gaza.”

Ministan na Isra’ila yana magana ne a kan tsohon kwamandan kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas da ke Zirin Gaza, Mohammed Deif, wanda gwamnatin kasar ta sanar da kashe shi a watan Janairu.

Katz ya kuma ce yuwuwar nasarar kisan gillar da gwamnati ta yi kan al-Houthi zai iya tunawa da kisan gillar da Tel Aviv ta yi wa tsohon babban sakataren kungiyar Hizbullah Sayyed Hassan Nasrallah, da kuma kisan Ismail Haniyeh, wanda shi ne shugaban ofishin siyasa na Hamas da Yahya Sinwar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments