Rundunar sojin haramtacciyar kasar Isra’ila (IOF) ta sanar a yammacin jiya Lahadi cewa an kashe wasu sojojinsu biyu a lokacin da aka kai wa tankar su hari a arewacin Gaza. Bugu da kari, an gano sojojin yahudawan da suka halaka a kudancin yankin na Gaza.
Dukkan sojojin biyu dai sun kasance mambobi ne na bataliya ta 129 da ke cikin runduna ta 8 da ke rike da makamai kamar yadda sojojin Isra’ila suka bayyana.
A halin da ake ciki kuma, kafofin yada labaran Isra’ila sun ba da rahoton tarwatsewar wani gini da sojojin yahudawan Sahyuniya da dama a cikinsa zirin Gaza. Rahotanni daga baya sun bayyana cewa wani jirgin sama mai saukar ungulu na soji ya isa asibitin Shaare Zedek da ke birnin al-Quds dauke da wasu da dama da suka samu raunuka sakamakon hakan.
Wannan dai na zuwa ne jim kadan bayan da rundunar sojin Isra’ila ta bayar da rahoton mutuwar sojoji da jami’ai 8 sakamakon wani harin bam da ake sa ran ‘yan gwagwarmayar Falastinawa suka kai shi a yankin Tell al-Sultan da ke Rafah a kudancin zirin Gaza. Daga cikin wadanda suka mutu har da mataimakin kwamandan wani kamfani a bataliya ta 601 ta Injiniya.
Bugu da kari, an kashe wani kwamandan sojin Isra’ila mai mukamin Manjo, tare da wasu sojoji uku a kudancin Gaza kwanakin baya.
Adadin sojojin Isra’ila da suka mutu tun fara yakin Gaza a ranar 7 ga watan Oktoba ya karu zuwa 661. Wannan ya hada da sojoji 311 da aka kashe tun fara kai farmakin kasa a Gaza. Bugu da kari, sojoji 3,617 ne suka samu raunuka, a cewar alkaluman da rundunar sojin Isra’ila ta fitar.