Rahotanni sun bayyana cewa firaministan Isra’ila Banjamen Natanyaho ya fadi a jiya juma’a cewa gwamnatin tel aviv ta amince da Somaliland a matsayin kasar mai cin gashin kai kuma sun rattaba hannu kan yarjejniyar kulla kyakkawar alaka tsakaninsu,
Abdirrahman Mohamed Abdullahi wanda ya sanar da kansa a matsayin shugaban yankin na Somaliland ya jinjinawa gwamnatin tel aviv na matakin da ta dauka a wannan lokacin mai cike da tarihi da za su kulla kyakkyawar dangantaka ta yin aiki tare tsakanin bangarorin biyu
wannan mataki ya fuskancin yin tofin Allah tsine daga ma’aikatar harkokin wajen kasar somaliya, masar, turkiya, da kuma kasar Djibouti wanda acikin bayannan da suka fitar sun yi watsi baki daya da wannan sanarwar da gwamnatin Isra’ila ta fitar .
Tuni dai ministan harkokin wajen kasar masar Badr abdel Aaty ya tattaunawa ta wayar tarho da takwarorinsa na kasashen Somaliya turikiya, da Djibouti kan batun da kuma sanarwa da Isra’ila ta fitar na amincewa da yankin Somali landa a matsayin kasa mai yanci.