Isra’ila Ta Sabawa Yarjejeniyar Sulhu Da Kungiyar Hizbullah

Sojojin Isra’ila sun kai hare-hare ta sama kan kasar Labanon a wani mataki na karya yarjejeniyar tsagaita bude wuta da kungiyar Hizbullah. Kamfanin dillancin labaran

Sojojin Isra’ila sun kai hare-hare ta sama kan kasar Labanon a wani mataki na karya yarjejeniyar tsagaita bude wuta da kungiyar Hizbullah.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya rawaito daga tashar al-Mayadeen ta cewa, an kai hare-hare ta sama a wajen yankunan Houmine al-Fowqa da Deir al-Zahrani da ke lardin Nabatie da ke kudancin kasar Lebanon.

Rahoton ya kara da cewa hare-haren na Isra’ila sun kuma auka kan garin Janta da ke lardin Bekaa na gabashin kasar Lebanon.

A halin da ake ciki kuma, rundunar sojojin mamaya ta ce ta kai hari kan wuraren da kungiyar ta Hizbullah, da suka hada da harba makamin roka, da wani wurin soji da ba a fayyace ba, da kuma hanyoyin da ke kan iyakar Syria da Lebanon.

Isra’ila ta kuma kai hare-hare ta sama a garuruwan Kfar Kila da Aita al-Shaab da ke yankin Nabatieh.

An kuma bayar da rahoton wani hari da jiragen yakin Isra’ila suka kai a wajen garin Jabal al-Botm da ke lardin Kudancin kasar Lebanon.

Bugu da kari, sojojin mamaya sun kutsa cikin garuruwan Maroun al-Ras, al-Majdiyeh, Wadi Khansa, da kuma Mari Plain na kasar Lebanon, a cewar al-Mayadeen.

A ranar 27 ga watan Nuwamba, 2024, ne aka cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra’ila da Hisbullah.

Yarjejeniyar wacce za ta kare a ranar 26 ga watan Janairu, ta bai wa Isra’ila wa’adin kwanaki 60 da ta janye dakarunta daga yankunan da ta mamaye tare da mika ragamar iko wuraren ga sojojin Lebanon da dakarun wanzar da zaman lafiya na MDD.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments