Hukumar dake kula da wuraren addini a Palasdinu ta sanar da cewa a cikin shekarar da ta gabata 2024 HKI ta rushe masallatan da adadinsu ya kai 966,wasu masallatan baki daya, wasu kuma rabi da rabi. Rushe masallatan dai yana tafiya ne kafada da kafada da yi wa Falasdinawa kisan kiyashi.
Masallatan da ‘yan sahayoniyar su ka rushe baki daya sun kai 815, sai kuma wasu 151 da su ka rusa wani bangare nasu.
Haka nan kuma sojojin mamayar sun rusa makabartu 19 baki daya, sai kuma majami’un kiristoci 3, duk a ciki zirin Gaza.
A can yammacin Kogin Jordan kuwa, cibiyar dake kula da wuraren addinin ta Falasdinawa ta ce, sau 256 ‘yan share wuri zauna suna yin kutse cikin masallacin Kudus tare da yin ibada irin ta yahudanci a cikin masallacin.
Ministan harkokin tsaron cikin gida na ‘yan sahayoniya mai tsattsauran ra’aui Itmar Bin Gafir kadai ya kutsa cikin mallasacin har sau 7 tun da ya hau wannan mukamin. Haka kuma tun fara yakin Gaza ya shiga sau 4.
Rahoton ya kuma bayyana cewa adadin ‘yan share wuri zauna da su ka shiga cikin farfajiyar masallacin na Kudus, a shekarar da ta gabata ta 2024,sun kai 2,567.
A can masallacin Annabi Ibrahim da yake birnin Khalil a kudancin yammacin kogin Jordan kuwa sau 674 ‘yan mamaya su ka hana a yi kiran salla, sannan kuma sun rufe masallacin da hana masu salla shiga har sau 10.
Adadin sojojin mamaya da su ka ci zarafin masu salla a masallacin sun kai 3,381,kamar yadda rahoton ya bayyana.