Kafofin yada labarai a Gaza sun ce hare-haren Isra’ila a zirin, sun kashe kimanin yara 70 a cikin kwanaki biyar da suka gabata.
Wannan a cewar rahoton na daga cikin 5,000 da aka kashe ko kuma suka bace a hare-haren da Isra’ila ke ci gaba da kaiwa a arewacin Gaza cikin kwanaki 100 da suka gabata.
Wata majiyar lafiya ta shaida wa Al Jazeera a ranar Lahadin da ta gabata cewa wasu Falasdinawa 9,500 sun jikkata a harin da sojojin Isra’ila suka kai a arewacin kasar da aka kaddamar a farkon watan Oktoba.
Ofishin yada labarai na gwamnatin Gaza ya kira harin da Isra’ila ta kai a matsayin “mafi muni.
Masu aiko da rahotanni sun ce arewacin Gaza a yanzu ya zama “’’kango’’
Isra’ila ta kaddamar da yakin kisan kare dangi a Gaza a watan Oktoban 2023.
Ya zuwa yanzu ta yi sanadin mutuwar mutane 46,565 tare da jikkata wasu sama da 109,000.