Isra’ila ta kashe ‘yan jarida 56 a cikin shekarar 2025

Akalla ‘yan jarida 128 ne aka kashe a duniya a shekarar 2025, yayin da fiye da rabin wadanda aka sun mutu ne a yankin gabas

Akalla ‘yan jarida 128 ne aka kashe a duniya a shekarar 2025, yayin da fiye da rabin wadanda aka sun mutu ne a yankin gabas ta tsakiya, a cewar alkalumman da kungiyar ‘yan jarida ta duniya (IFJ) ta fitar wannan Alhamis.

Adadin ya nuna karuwa ne daga 2024 kuma yana nuna abin da hukumar ta bayyana a matsayin karuwar hadari ga rayuwar  ‘yan jarida a duniya.

“Wannan ba kididdiga ba ce kawai, jajircewa ce da sadaukarwa ta  abokan aikinmu,” babban sakatare na IFJ Anthony Bellanger ya shaida wa AFP.

Ya ce karuwar wadannan kashe-kashen na nuni da gazawar da aka samu wajen kare ‘yan jaridun da ke aiki a yankunan da ake yaki da kuma wuraren da ke fama da ake tabarbarewar  lamurran siyasa.

Kungiyar ta IFJ ta bayyana damuwarta ta musamman kan halin da ake ciki a yankunan Falasdinawa, inda ta tattara bayanan kashe ma’aikatan yada labarai 56 a shekarar 2025 a daidai lokacin da Isra’ila take ci gaba da yaki a Gaza duk da yarjejeniyar tsagaita wuta.

“Ba mu taba ganin wani abu makamancin haka ba: mace-mace da yawa a cikin kankanin lokaci, a irin wannan karamin yanki,” in ji Bellanger.

Bayan Gaza, an kuma kashe ‘yan jarida a kasashe da suka hada da Yemen, Ukraine, Sudan, Peru, da Indiya, wanda ke nuna irin barazanar da ma’aikatan yada labarai ke fuskanta a duniya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted