Kungiyar Hamas wacce take iko da zirin Gaza ta yi tir da kissan wani babban jami’in tsaro na cikin gida a yankin a wani hari da ta kai kan gidansa a yau Laraba, inda ta kashe shi da matarsa da kuma yayansu 2.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar Hamsa a Gaza na cewa, kissan Mohammad Abuluf ya nuna cewa isra’ila tana ci gaba da kissan kiyashi a gaza, irin kissan da ya haramta bisa dokokin kasa da kasa.
A safiyar yau Laraba ne, wasu makamanIsra’ila suka fada a kan gidan Mohammad Abu luf da ke unguwar Al-shati dake cikin birnin Gaza a bakin ruwa, inda suka kashe shi da matarsa da kuma yayansa biyu.
Labarin ya kara da cewa wannan yana faruwa ne a dai dai lokacinda ake cikin abinda suke kira yarjeniyar zaman lafiya. Wannan Isra’ila bata taba mutuntashi bat un lokacin da aka rattaba mata hannu a cikin watan Octoban shekara ta 2025.
Mafi yawan manya manyan kasashen duniya sun yi shiru kan abinda yake faruwa a Gaza, na hana kayakin agaji isassu ciga yankin da kuma ayyukan jinkai.