Rahotanni sun bayyana cewa sama da falasdinawa malaman makaranta 800 ne suka mutu tare da jikkata sama da 3300 daga lokacin da isra’ila ta kaddamar da yakin kare dangi kan alummar gaza a watan oktoban shekara ta 2023 kamar yadda ma’aikatar ilimi ta yankin gaza ta sanar
A cikin wani bayani da aka fitar game da ranar malamai ta duniya wato 5 ga watan oktoba ma’aikatar ilimin ta ce sama da mutane 170 ne ake tsare da su ,yace harkar ilimi a fadin yakin falasdinu na fuskantar babbar matsalar ci gaba da rayuwa, domin kare hakkin ilimi a daidai lokacin da isra’ika ke ci gaba da kai hare hare da kuma kuntatawa
Ma’aikatar ilimin ta ce bangaren ilimi a yankin gaza da gabar yammacin kogin Jodan yana fuskantar mummunar barna da rushe rushe , yayin da su kuma mlamai ke fuskantar takurawa da matsin lamba da razanarwa a wuraren binciken ababen hawa musamman a masafer yatta dake kudancin Khalil a tsakiyar yammacin kogin jodan da sauran yankuna.
Ma’akatar ta yi kira ga majalisar dinkin duniya da sauran masu fada a ji na duniya da bangarorin ilimi da kungiyoyin kare hakkin dana dama da su dauke mataken gaggawa domin kare dalibai da ilimi a yankin da ake neman kawo karshensa da karfin tsiya