Isra’ila Ta Kashe Mutane 10 A Wani Hari Da Ta Kai A Birinin Damaskas Na Kasar Siriya

Rahotanni sun bayyana cewa Isra’ila ta kai hari ne a garin beit Jin dake gefen birnin damaskas da ya kai ga mutuwar mutane 10 yayin

Rahotanni sun bayyana cewa Isra’ila ta kai hari ne a garin beit Jin dake gefen birnin damaskas da ya kai ga mutuwar mutane 10 yayin da wasu da dama kuma suka jikkata,

wannan ya faru ne bayan rikici da ya barke tsakanin mazauna yankin da kuma sojojin Isra’ila da ya kai ga jikkata sojoji 6 .

yawan kai hare-hare da Isra’ila ke yi yana nuna irin zaman dar-dar da ake ciki a kudancin kasar siriya  musamman a damaskas da Qunaitara, kuma wannan hari wani bangare ne na mataken da sojojin isra’ila ke dauka wuraren sojojin kasar siriya da hakan kara jefa farare hula cikin fargaba da rashin kwanciyar hankali.

Rahotanni sun bayyana cewa sojojin Isra’ila suna ci gaba da tunkarar mazauna garin Beit Jin da hakan ya kai ga jikkata sojojin isra’ila guda 6, wanda haka yasa Isra’ila ta yi ruwan bama –bamai a yanki, da ya kai ga mutuwar mutane 10. a lokacin guda kuma isra’ila ta harba makamai a gabashin garin tel ahmar dake yankin qunaitara, da hakan ke nuna karuwar ayyukan soji a wajen.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments