Isra’ila Ta Kashe Karin Falasdinawa 40 A Cikin Sa’o’I 24 Da Suka Gabata

Ma’aikatar lafiya a Gaza a sanar da cewa adadin Falasdinawan da sukayi shahada sanadin hare-haren Isra’ila tun ranar 7 ga watan Oktoba ya haura zuwa

Ma’aikatar lafiya a Gaza a sanar da cewa adadin Falasdinawan da sukayi shahada sanadin hare-haren Isra’ila tun ranar 7 ga watan Oktoba ya haura zuwa Dubu 37 da Dari 834.

Ko a cikin sa’o’I 24 da suka gabata falasdinawa 40 suka rasa rayukansu sanadin hare-haren na Isra’ila a Gaza.

Ko baya ga wadanan alkalumman da akwai wasu Dubu 86 da Dari 858 da suka jikkata sanadin hare-haren da Isra’ila ke ci gaba da kaiwa a Zirin.

A wani labarin kuma ana ci gaba da zanga zangar goyan bayan falasdinu a sassan duniya tare da bukatar neman a tsagaita wuta a Gaza.

Ko a baya baya nan ma Dubban masu zanga-zangar goyon bayan Falasdinu ne suka fito kan titunan Vienna, babban birnin kasar Austria, domin nuna goyon bayansu ga al’ummar Gaza tare da yin Allah wadai da yakin da Isra’ila ke yi kan yankin da aka yi wa kawanya dake fuskantar hare-haren bama-bamai ba kakkautawa.

Masu zanga-zangar na dauke da tutocin Falasdinawa da tutoci na neman tsagaita bude wuta a Gaza, kamar yadda cibiyar yada labaran Falasdinu ta Turai ta yada a yanar gizo.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments