Search
Close this search box.

Isra’ila Ta Kashe Falastinawa Sama Da 70 A Cikin Kasa Da Sa’oi 24

Falasdinawa fiye da 70 ne suka yi shahada a cikin kasa da sa’oi 24 ad suka gabata, sakamakon hare-haren kisan kare dangin da Isra’ila take

Falasdinawa fiye da 70 ne suka yi shahada a cikin kasa da sa’oi 24 ad suka gabata, sakamakon hare-haren kisan kare dangin da Isra’ila take kan al’ummar Gaza, kamar yadda majiyoyin kiwon lafiya suka tabbatar.

Wani hari ta sama ya faɗa kan wani rukunin gida a unguwar Sheikh Radwan da ke arewacin Gaza, ya yi sanadin shahadar  mutum uku da jikkata da dama.

Haka kuma wani Bafalasɗine ya rasa ransa sakamakon wani makamin atilari da Isra’ilar ta harba a sansanin gudun hijira na Bureij.

Haka kuma ƙarin mutum biyu sun rasu a yayin wani harin makami mai linzami da Isra’ilar ta ku a Deir al Balah da ke tsakiyar Gaza, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutum biyu.

Aƙalla Falasɗinawa 63 aka kashe aka jikkata da dama a wasu jerin hare-haren Isra’ila ta sama da suka kai sassa da dama na Gaza da aka mamaye.

Asibitin Nasser da ke Khan Younis ya karbi gawawwakin Falasɗinawa 59.

Mahmoud Basal, mai magana da yawun Hukumar Tsaron Al’umma ta Falasɗinu ya faɗa a wata sanarwa cewa “wasu daga Falasdinawan da aka kashe a hare-haren na sama na Isra’ila da aka kai gidaje na iyalen Othman ne a Benayen Ain Jalut a sansanin ‘yan gudun hijira na Nuseirat a tsakiyar birnin Gaza.”

Ya kara da cewa, yankunan da ke gabashin birnin Deir al Balah da sansanin Nuseirat sun fuskanci ruwan makaman atilare na Isra’ila, bayan wa’adin da sojoji suka bayar na ficewa daga yanki mai girma na Deir al Balah a ranar Asabar da yamma.

Basal ya ƙara da cewa “makaman atilare na Isra’ila sun fi yawa a shataletalen Dawla, ya zarce zuwa layi na 8, ya kuma ƙarasa shataletalen Dahdouh (kudu maso yammacin Gaza).”

Ya bayyana cewa sojojin Isra’ila sun “dage wajen tsananin ƙonawa da rusa gine-ginen zama a kudancin Birnin Gaza.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments