Isra’ila ta kashe Falasdinawa kusan 100 a hare-haren da ta kai a Gaza

Kamfanin dillancin labarai na WAFA ya sanar da cewa, Isra’ila ta kashe akalla wasu Falasdinawa 98 a hare-haren da ta kai a yankin Gaza da

Kamfanin dillancin labarai na WAFA ya sanar da cewa, Isra’ila ta kashe akalla wasu Falasdinawa 98 a hare-haren da ta kai a yankin Gaza da ta yi wa kawanya a baya baya nan.

Hukumar ta ruwaito wasu majiyoyin lafiya na cewa an kai mutum 23 da lamarin zuwa asibitin Al-Shifa, 29 zuwa Asibitin Baftisma na Al-Ahli, 28 zuwa Asibitin Al-Awda, tara zuwa Nasser Medical Complex, sannan tara zuwa Asibitin Al-Aqsa.

Tun bayan da gwamnatin Isra’ila ta kaddamar da yakin kisan kare dangi a Gaza a ranar 7 ga watan Oktoban 2023, ta kashe Falasdinawa kusan 66,000 tare da raunata fiye da 167,000, yawancinsu mata da yara.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments