Isra’ila Ta Kashe Falasdinawa 4 A Wani Harin Da Ta kai A Yankin Gaza

A wasu sabbin hare-hare da isra’ila ta kai ta kashe falasdinawa guda 4 da kuma jikkata wasu na daban a yankin gaza a ci gaba

A wasu sabbin hare-hare da isra’ila ta kai ta kashe falasdinawa guda 4 da kuma jikkata wasu na daban a yankin gaza a ci gaba da keta yarjejeniyar dakatar da bude wuta da take yi da aka cimma tsakaninsu da kungiyar Hamas da Amurka ta jagoranta.

majiyar labaran yankin falasdinu ta bayyana cewa wani yaro dan shekara 17 da haihuwa ya rasu bayan da isra’ila ta kai hari a kusa da Al sanafour intersection a gabashin yankin gaza,

wasu karin mutane 2 su ma sun rigamu gidan gaskiya sakamakon hari da makamin mai linzami da isra’ila ta kai a kusa da garin Tuffa dake makwabtaka da bangaren arewacin gaza,  shi ma wani mutum guda ya mutu bayan harin kan mai uwa da wabi da sojojin isra’ila suka kai a yankin.

sojojin isra’ila na ci gaba da kai hari ta sama da ta kasa a fadin yankin Gaza da suka hada da Tuffah inda aka fusakanci hauhawan tashe-tashen hankula a yan kwanakin nan,  kuma sojojin isra’ila na ci gaba da rusa gidaje a kusa da abin da suka kira  layi mai launin ruwan kawai.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted