Rahotanni daga Lebanon na cewa Isra’ila ta kai wasu jerin hare-hare a Lebanon wanda ya nuna yadda ta ke ci gaba da keta yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya rawaito daga shafin sadarwa na yanar gizo na kasar Labanon cewa, sojojin na Isra’ila sun kaddamar da hare-haren bama-bamai guda biyu a garin Meiss el-Jabal da ke kudancin kasar a jiya Lahadi.
Hare-haren na zuwa ne sama da wata guda bayan da Isra’ila ta amince da yarjejeniyar tsagaita bude wuta da kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon.
A garin Khiam da ke kudancin kasar, hukumar tsaron farar hula ta Lebanon ta sanar da gano gawarwakin mutane biyar da aka kashe a harin da Isra’ila ta kai, inda ta ce za a ci gaba da kokarin gano daukacin mutanen da suka bata nan da mako mai zuwa.
Hare-haren da Isra’ila ke kaiwa Lebanon sun yi sanadiyar mutuwar mutane akalla 3,961 da wasu 16,520 tun lokacin da aka fara yakin Gaza.