Isra’ila ta sanar a yammacin yau Talata cewa, ta kai wani hari kan wani gini a birnin Beirut, na kasar Lebanon, inda suka auna wani kwamandan kungiyar Hezbolla da suka ce shi ne ya kai harin ranar Asabar a tuddan Golan.
A cikin wata sanarwa da rundunar sojin Isra’ilar ta fitar, ta ce “Sojojin Isra’ila sun kai hari a Beirut kan kwamandan da ke da alhakin kisan ‘ya’yan Majdal Shams inda aka kashe matasa 12, harin da kungiyar Hezbollah ta musanta.
Tunda farko dai rahotanni sun ce Isra’ila da kungiyar Hizbullah sun yi musayar wuta mai muni, bayan harin roka da aka kai duk da kiraye-kirayen kai zuciya nesa da ake musu.
Likitocin Isra’ila sun ce an kashe wani mutum mai shekaru 30, bayan wani harin roka da aka kai a arewacin HaGoshrim.
A baya-bayan nan dai Isra’ila ta bayyana cewa, ta kai hare-hare kimanin 10 kan mayakan Hizbullah a cikin dare a yankuna bakwai daban-daban na kudancin kasar Lebanon, inda suka kashe daya daga cikin mayakan kungiyar.