Isra’ila Ta Kai Hari A Birnin Beirut Na Kasar Lebanon

Isra’ila ta sanar a yammacin yau Talata cewa, ta kai wani hari kan wani gini a birnin Beirut, na kasar Lebanon, inda suka auna wani kwamandan kungiyar Hezbolla da suka ce shi ne ya kai harin ranar Asabar a tuddan Golan.  A cikin wata sanarwa da rundunar sojin Isra’ilar ta fitar, ta ce “Sojojin Isra’ila […]

Amurka Ta Kakabawa Iran Sabbin Takunkumai

Amurka ta sanar da kakabawa Iran sabbin takunkumai. Ma’aikatar kudi ta Amurka ta kakaba sabbin takunkuman ga sassa masu ruwa da tsaki wajen samar da kayayyakin kera makami masu linzami da jiragai marasa matuka na Iran. Shafin yanar gizo na ma’aikatar baitul malin Amurka ya sanar yau cewa ofishin mai kula da kadarorin waje (OFAC) […]

Mutane Kusan 300 Isra’ila Ta Kashe A Farmakin Khan Yunis

Hukumar kare fararen hula ta Gaza ta ce farmakin da Isra’ila ta kai a Khan Yunis da kewaye ya kashe mutane kusan 300 a cikin ‘yan kwanakin nan. Kakakin hukumar Mahmud Bassal ya fada a ranar Talata cewa adadin shahidai a Khan Younis ya zarce yadda aka yi tsammani tun farko, inda aka tabbatar da […]

Pezeshkian, Ya Yi Rantsuwar Kama Aiki A Matsayin Shugaban Iran Na 9

Shugaban Iran Masoud Pezeshkian ya yi rantsuwar kamai aiki a gaban majalisar dokokin kasar, a bikin da aka shirya tare da halartar manyan baki da yammacin yau Talata. Bayan shan rantsuwa bisa kur’ani mai tsarki, Pezeshkian ya lashi takobin kare addinin musulunci da na Jamhuriyar Musulunci da kuma kundin tsarin mulkin kasar. “A matsayina na […]

Aljeriya Ta Ba Da Sanarwar Janye Jakadanta A Faransa Nan Take

Gwamnatin Aljeriya ta sanar da janyewar jakadanta a Faransa nan take. Ma’aikatar harkokin wajen kasar a cikin wata sanarwa da kamfanin dilancin labaren APS ya rawaito, ta ce daga yau Talata “mai kula da harkoki ne zai kula da al’amuran diflomatsiyya a kasarta faransa. Tun a ranar 25 ga watan Yuli ne, Ma’aikatar Harkokin Wajen […]

Kasashen Iran Da Gambiya Sun Dawo Da Alakar Diflomasiyya A Tsakaninsu

An samu kyautatuwar alaka da dawo da dangantakar diflomasiya tsakanin kasashen Iran da Gambiya A jiya litinin ne mai kula da ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Ali Baqiri ya karbi bakwancin ministan harkokin wajen kasar Gambiya, kuma a yayin ganawar jami’an biyu, mai kula da ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran da ministan harkokin wajen kasar […]

Majalisar Dinkin Duniya Ta Ce: Zirin Gaza Na Cikin Mummunan Yanayi A Halin Yanzu

Majalisar Dinkin Duniya ta ce: Zirin Gaza na cikin wani mummunan yanayi ta fuskar cututtuka, kashe-kashen rayukia, raunuka da hasarar rayuka Babbar jami’ar kula da ayyukan jin kai da sake gina yankin Zirin Gaza, Sigrid Kaag ta bayyana cewa: Zirin Gaza ya kai wani sabon mataki mai ban tsoro da muni dangane da raɗaɗi, barna, […]

Babban Sakataren MDD Ya Taya Zababben Shugaban Iran Murnar Kan Nasarar Zabensa

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya taya zababben shugaban kasar Iran murna tare da bayyana shiri Majalisarsa na hadin gwiwa da sabuwar gwamnatin Iran A cikin wata sakon wasika da ya aikewa zababben shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian, babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, António Guterres, ya taya shi murnar zaɓen da aka yi masa a […]

Pezeshkian: Taimakawa Gwagwarmayar Yaki Da Isra’ila Wajibi Ne Na Shari’a A Kan Iran

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya tabbatar da goyon bayan Jamhuriyar Musulunci ta Iran ga kungiyoyin gwagwarmaya, sannan kuma ya yaba da irin rawar da suke takawa a kasashen Labanon da Palastinu, yayin ganawarsa da mataimakin babban sakataren kungiyar Hizbullah Sheikh Naim Qassem da Sakatare Janar na kungiyar Islamic Jihad, Ziad Al-Nakhalah, a ziyarar da […]

Hezbollah Ta Ragargaza Wasu Gine-Ginen Sojin Isra’ila

Kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ta kaddamar da wasu munanan hare-hare na mayar da martani ga hare-haren wuce gona da irin da Isra’ila ke kai wa kan kasar Labanon, tare da jaddada goyon bayanta ga Falasdinawa a Gaza. Harin farko da aka kaddamar a ranar jiya  litinin, an ga mayakan Hezbollah sun harba makaman roka […]

Duniya Na Ci Gaba Da Sukar Isra’ila Kan Laifukan Yaki A Gaza

Isra’ila na fuskantar sabuwar suka game da aikata laifukan yaƙi bayan an fitar da wasu sabbin bidiyoyi da ke nuna yadda dakarunta suke lalata wata ma’ajiyar ruwan sha a kudancin Gaza, tare da wasu rahotanni da suka nuna yadda sojojinta suka yi fyaɗe ga wata Bafalasɗiniya fursuna a gidan yari da ke Negev Desert. Wani […]

Tinubu Ya Sa Hannu Kasn Dokar Fara Biyan Sabon Albashi

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sanya hannun kan dokar fara biyan N70,000 a matsayin albashi mafi karanci ga ma’aikata a Najeriya. A ranar Litinin shugaban kasan ya rattaba hannu kan sabuwar dokar karin albashin a lokacin taron Majalisar Zartaswa ta Kasa (FEC), wanda Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio da sauran jagoroin bangaren majalisa suka […]

Pezeshkian Ya Gargadi Isra’ila Kan Gigin Shiga Wani Sabon Yaki Da Lebanon

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya yi gargadin cewa gwamnatin Isra’ila za ta fuskanci mummunan martani idan ta yi gigin kai wa kasar Lebanon hari. Sabon shugaban na Iran ya yi wannan gargadin ne a wata tattaunawa ta wayar tarho da ya yi da takwaransa na Faransa Emmanuel Macron a ranar Litinin. Pezeshkian ya bayyana […]