Isra’ila ta kai hari kan ababen more rayuwa na fararen hula a Yemen

Isra’ila ta kaddamar da wani farmaki ta sama a kan babban birnin kasar Yemen Sanaa a jiya Lahadi, inda ta kai hare-hare a yankin kudu

Isra’ila ta kaddamar da wani farmaki ta sama a kan babban birnin kasar Yemen Sanaa a jiya Lahadi, inda ta kai hare-hare a yankin kudu maso gabashin birnin San’a.

Wakilin tashar Almayadeen ya bayyana cewa, Isra’ila ta kai harin ne kan wani gidan mai  a kudu maso gabashin birnin San’a mallakin kamfanin mai na kasar Yemen da ke kan titin Al-Sitteen, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane  tare da jikkata wasu da dama a lokacin da suke shan mai a motocinsu da sauran ababen hawa a wurin.

Kamfanin mai na kasar Yemen ya kuma tabbatar da cewa al’amura sun daidaita an kuma shawo kan gobarar da ta tashi a wurin, tare da kwantar da hankalin ‘yan kasar, kamar yadda wakilin Almayadeen ya bayyana.

Da yake magana daf da wurin da abin ya faru, mai magana da yawun kamfanin mai na kasar Yemen Essam al-Mutawakel, ya bayyana cewa, Isra’ila tare ad masu mara mata baya suna kai hari kan ababen more rayuwar jama’a faren hula ne da sunan yunkurin murkushe dakarun Yemen da ke kai musu hare-haren daukar fansa kan kisan kiyashin Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments