Majiyar sojojin kasar Yamen sun sanar cewa a ci gaba da hare-haren wuce gona da iri da HKi ke yi, Jiragen yakin HKI sun kai hari kan tashar jirgin ruwan hudaidai dake kasar kuma sun samu nasarar kakkabo makaman.
Kakakin sojin kasar yamen yahya Saree ya fadi a cikin shafinsa na x cewa makaman kariya da muke dasu sun kalubalanci hare haren da Isra’ial ta kai a tashar jirgin ruwa na Hudaida, Isra’ila ta harba makamai masu linzami 12 a tashoshin jiragen ruwanta guda 3.
Gidan rediyo isra’ila ya sanar cewa babban dalilin kai harin shi ne don a hana gudanar da ayyuka na tsawon makwanni, bayan gyara wuraren da suka lalace a hare-haren baya bayan nan da aka kai,
Da Saniya safiye ne sojojin Isra’ila suka sanar da a kawashe tashar jirgin ruwa ta Hudaida inda suka yi barazanar kai hari a tashar a yau.