Akalla Falsdinawa 78 Ne Suka Yi Shahada A Yau A Gaza.

Yakin da aka kwashe fiye da shekara ana yi yankin zirin Gaza ya haifar da mummunar asara rayukan fararen hula, yayin da lamura ke ci gaba da dagulewa a yankin inda Isra’ila ke ci gaba da kisan kare dangi ta hanyar kai hare-hare ta sama da kasa da kuma tana amfani da yunwa a matsayin […]
Isra’ila Ta Kai Hari A Tashar Jirgin Ruwan Hudaida Dake Yamen

Majiyar sojojin kasar Yamen sun sanar cewa a ci gaba da hare-haren wuce gona da iri da HKi ke yi, Jiragen yakin HKI sun kai hari kan tashar jirgin ruwan hudaidai dake kasar kuma sun samu nasarar kakkabo makaman. Kakakin sojin kasar yamen yahya Saree ya fadi a cikin shafinsa na x cewa makaman kariya […]
Iran Ta Gabatar Da Sabbin Kayayyaki 5 A Wajen Taron kere-kere .

Rahotanni sun bayyana cewa kasar iran ta bayyana sabbin kayayyaki guda 5 da ta kera a wajen babban taron kere-kere na kasa da kasa karo na 23,kuma dukkansu kamfanonin kasar iran ne suka yi su domin rage dogaro da kayyakin kasashen waje. Taron ya samu halartar mataimakin shugaban hukumar kula da kimiya da fasaha ta […]
Iran Ta Bukaci IAEA Tayi Tir Da Harin Da Isra’ila Ta Kai A Tashoshin Nukiyarta.

Mohammad Islami shugaban hukumar kula da makamashin nukiliya na Iran ta fadi a bayan taron da hukumar ta IAEA dake gudanarwa a Vienna yanzu haka cewa yana neman hukumar ta IAEA ta goyi bayan kudurin da ta fitar kuma ta yi Tir da harin wuce gona iri da hki ta kai kan tashoshin nukiliyarta. Wakilai […]
Jonathan Zai Jagoranci Taron Tattaunawa Kan Dimokuraɗiyya A Ghana

Tsohon Shugaban Ƙasar najeriya, Goodluck Jonathan, ya isa birnin Accra, na Ƙasar Ghana, domin halartar taron Democracy Dialogue na 2024 da Gidauniyarsa ta shirya tare da hadin gwiwar gwamnatin kasar. Taron na bana, mai taken “Dalilan Da Ke Sa Dimokuraɗiyya Ta Mutu”, zai hada shugabanni da masana don tattauna ci gaba, kalubalen, da makomar dimokuradiyya […]
Pezeshkian: Saudiyya Na Iya Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Samar Da Hadin Kan Kasashen Musulmi

Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Saudiyya na iya taka muhimmiyar rawa wajen hadin kan kasashen musulmi Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya jaddada cewa: Gwamnatin sahayoniyya ba za ta kuskura ta kai hari ko kai wa wata kasa ta Musulunci hari ba matukar kasashen musulmi suka hade kansu; kuma Saudiyya za ta iya taka […]
Pezeshkian: Ta’addancin Haramtacciyar Kasar Isra’ila Kan Kasar Qatar Zalunci Ne Ga Diflomasiyya

Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Ta’addancin yahudawan sahayoniyya kan Qatar zalunci ne ga diflomasiyya Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa: Harin wuce gona da iri kan kasar Qatar, wani hari ne da kungiyar yahudawan sahayoniyya ta shirya kai wa, da nufin dakile yunkurin diflomasiyya na kawo karshen kisan kiyashin da ake yi […]
Baqa’i: Kowace Kasa A Duniya Tana Da Hakkin Mallakar Makamashin Nukiliya Na Zaman Lafiya

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya tabbatar da haƙƙin kasashe na haɓakawa da amfani da makamashin nukiliya na zaman lafiya Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Isma’il Baqa’i, ya yi ishara da shawarar da Iran ta gabatar na daftarin kudurin da ya haramta kai hare-hare kan cibiyoyin makamashin nukiliyar kasashe masu zaman lafiya, […]
Kungiyar Human Rights Watch; Isra’ila Ta Kashe ‘Yan Jarida Fiye Da 30 A Kasar Yemen Ne Da Gangan

Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Human Rights Watch ta ce: Laifin da Isra’ila ta yi na kashe ‘yan jaridun Yemen babban ta’addanci ne Kungiyar kare hakkin bil’ adama ta Human Rights Watch ta tabbatar da cewa: Harin da yahudawan sahayoniyya suka kai a ranar 26 ga watan Satumba kan ‘yan jaridun kasar Yemen, wanda ya […]
Kungiyar Kare Hakkokin Bil’Adama Ta Siriya Ta Bankado Karin Fararen Hula Da Aka Kashe A Rikicin Suweida

Kungiyar Kare Hakkokin Dan Adam ta Siriya ta bayyana sabbin mutanen da suka mutu sakamakon harin Suweida Kungiyar kare hakkin dan adam ta Siriya (SOHR) ta bayyana wasu sabbin fararen hula tara da aka ci zarafinsu a lokacin abubuwan da suka faru a Suweida a watan Yulin da ya gabata. Hukumar da ke sa ido […]
Tawagar Yan Wasan Damben Gargajiya Ta Iran Ta Zama Zakara A Damben Ta Duniya

JMI ta zama zakara a gasar damben girgajiya ta kasa da kasa bayan ta fara shiga gasar shekaru 12 da suka gabata . Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi yana taya tawagar yan damben murna da nasarar da suka samu, ya kumakara da cewa wannan […]
An Fara Taron Hukumar Makamashin Nukliya Ta Duniya IAEA Karo Na 69 A Birnin Vienna

An fara taron hukumar IAEA ta kasa da kashe karo na 69TH a jiya Litinin, a birnin Vienna inda a taron ne ake fayyana al-amura masu muhimmanci da suka shafi makamashin Nukliya a duniya, kuma tuni shugaban hukumar makamashin Nukliya ta kasar Iran Muhammad Eslami yake jagorantar tawagar Iran a taron. Kamfanin dillancin labaran IP […]
Espania Ta Soke Cinikin Makamai Na EUR Miliyon 700 Da HKI Saboda Kissan Kiyashi A Gaza

Gwamnatin kasar Spaine ta soke kontaragin sayan makama daga HKI wadanda yawansu ya kai Euro Miliyon 700, saboda kissan kiyashin da ke faruwa a gaza. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa a jiya Litinin ne gwamnatin firay minister Pedro Sanchez ta bada wannan sanarwan ta kuma kara da cewa makaman su […]
Makaman ‘Drons’ Na Yemen Sun Fada Kan Wurare Masu Muhimmanci A HKI

Jaragen yaki wadanda ake sarrafasu daga nesa wato Drones sun fada kan wurare masu muhimmanci a kudancin kasar Falasdinu da aka mamaye, yan sa’o’in da suka gabata. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto kakakin sojojin kasar Yemen Burgediya Janar Yahyah Saree yana fadar haka a dazo-dazon nan .Ya kumakara da cewa. hare-haren […]
Taron Doha: Daga matakin Allawadai zuwa matakan kalubalantar laifukan Isra’ila

Babban daraktan kamfanin dillancin labaran kasar Qatar ya bayyana cewa taron gaggawa na kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC da ke tafe yana nuni da wani muhimmin sauyi na hadin kan kasashen larabawa da musulmi dangane da laifukan da ake aikatawa kan al’ummar Palastinu. A cewar Pars Today, dukkanin idanuwa a ranakun Lahadi da […]
Ministan Tsaron Venezuela Ya Gargadi Amurka Game Da Yunkurin Juyin Mulki A Kasar

Ministan tsaro na kasar Venezuela Vladimir Padrino López ya gargadi gwamnatin Amurka dangane da duk wani kokari na kaiwa kasar Venuzuela hare hare saboda kifar da gwamnatin shugaba Nicolas Madoro. Tare da fakewa da fasakorin kwayoyi. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Vladimir yana cewa take-taken gwamnatin Amurka na sojojin da ta […]
Pezeshkian: Ya kamata kasashen musulmi su yanke alaka da gwamnatin sahyoniya

Shugaban kasar Iran yana mai jaddada cewa wajibi ne kasashen musulmi su karfafa hadin kai da hadin kai don mayar da martani ga ayyukan gwamnatin sahyoniyawan, inda ya ce: Wajibi ne kasashen musulmi su tsaya tsayin daka tare da daukar matakai na zahiri a fagen tattalin arziki, al’adu da zamantakewa, yanke alakarsu da gwamnatin sahyoniyawan. […]