Jiragen yaki isra’ila sun yi ruwan bama- bamai a filin saukar jiragen sama na sojoji a kasar siriya a yau talata yan sa’oi bayan ziyara da dakarun sojin kasar Turkiya suka kai wajen domin duba halin da yake ciki.
Majiyar labarai ta tsaro da ta bukaci a sakaya sunanta ta bayyana cewa harin da isra’ila ta kai ya lalata titin filin jirgin soji na Abu al-Duhur dake kusa da garin Idlib, kuma yayi mummunar barna a wajen sai dai babu rahoto game da wanda ya jikkata,
filin saukar jiragen sama na soji na Abu Adhuhur yana da nisan kilo mita 50 da kudu masu yammacin birnin Aleppo, akalla kilomita 300 daga cikin HKI, kuma motocin sojin kasar turkiya suna wajen a lokacin da aka kai harin,
Isra’ila tana kokarin kange kasar turkiya daga duk wani yin tasiri a kasar siriya, a baya ta kai hari ne don jan kunne Ankara game da duk wani yunkuri na taimakawa kungiyar hay’ati tahrir al-sham wajen sake gina filin jirgin saman
tun bayan faduwar tsohuwar gwamantin bashar Assad a farkon watan decemba shekara ta 2024 isra’ila ta kaddamar da hare-hare a sansanonin soji da wuraren aiki da kuma wajen adana kayan soji da siriya ke sarrafawa a da .