Isra’ila Ta Kai Hare-hare A Wasu Wuraren Soji A Kasar Siriya 

Kafar yada labaran Syria ta ce Isra’ila ta kaddamar da hare-hare ta sama a wasu sassa na tsakiya da kuma yammacin kasar. Rahotanni sun ce

Kafar yada labaran Syria ta ce Isra’ila ta kaddamar da hare-hare ta sama a wasu sassa na tsakiya da kuma yammacin kasar.

Rahotanni sun ce an kai hare haren ne a kusa da Homs da Palmyra da kuma birnin Latakia da ke gabar ruwa. Ana ganin Isra’ilan ta kai hare-haren kan sansanonin Soji ne.

Ba a bayar da rahoto akan mutanen da hare haren ya shafa ba, haka ita ma Isra’ilan ba ta ce komai a kan harin ba.  Isra’ila dai na kai hare-hare ta sama tun bayan hambarar da gwamnatin shugaba Bashar al- Assad a watan Disambar bara.

ana ta bangaren gamnatin kasar siriya ta tir da kai harin tare da bayyana shi a matsayin keta dokokin kasa da kasa, da ma na majalisar dinkin duniya. Tun bayan kifar da gwamnatin Bashar Assad HKI take ci gaba da kai hare-haren kan wuraren soji da dukkan wuraren da e da alaka da su.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted