Aragchi Ya Gana Da Grrosi da Kuma Takwaransa Na Kasar Masar

Ministan harokokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya gana da tokwaransa na kasar Masar da kuma shugaban hukumar makamashin nukliya ta duniya Rafael Grossi a karon farko tun bayan yakin kwanaki 12 wanda kasashen Amurka da HKI suka kaiwa Iran a cikin watan yunin da ya gabata. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya […]

Isra’ila Ta Kai Hari Kan Jagororin Hamas A Doha

Jiragen yakin HKI sun kai hare-hare kan cibiyar gudanarwa na kungiyar Hamas dake birnin Doha na kasar Qatar dazo da rana. Tashar talabijan ta Presstv a Tehran ta nakalto tashar talabijan ta 13 ta Haramtacciyar Kasar Isra’ila na bada labarin cewa jiragen yahudawan sun kai hare-haren ne a dai-dai lokacinda shuwagabannin kungiyar Hamas suke taro […]

Kasashen Larabawa Da Na Duniya Sun Yi Allawadai Da Harin Isra’ila Doha

Kasashen larabawa da kungiyoyin kasa da kasa da wasu kasashen duniya sun yi tir da hare-haren da HKI ta kai kan birnin Doha babban birnin Qatar a kokarinta na kashe shuwagabannin kungiyar Hamasa a yau Talata. Tashar talabijin ta Almayadeen ta kasar Lebanon ta bayyana cewa babban sakataren MDD Antonio Gotterre ya yi tir da […]

Iran Da Masar Sun Tattauna Kan Gaza Da Shirin Iran na Nukiliya

Rahotanni sun bayyana cewa ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya tattauna da takwaran aikinsa na kasar masar badar albadelatty ta wayar tarho inda suka tattauna game da batutuwan da suka shafi yankin da kuma irin ci gaban da aka samu, kuma sun mayar da hankali kan batutuwan da suka shafi Gaza da kuma […]

Isra’ila Ta Kai Hare-hare A Wasu Wuraren Soji A Kasar Siriya 

Kafar yada labaran Syria ta ce Isra’ila ta kaddamar da hare-hare ta sama a wasu sassa na tsakiya da kuma yammacin kasar. Rahotanni sun ce an kai hare haren ne a kusa da Homs da Palmyra da kuma birnin Latakia da ke gabar ruwa. Ana ganin Isra’ilan ta kai hare-haren kan sansanonin Soji ne. Ba […]

Hamas Ta Yi Tir Da Gazawar MDD Kan Kisan Kare Dangin Isra’ila A Gaza

Kungiyar gwagwarmaya ta Hamas ta yi tir da shiru da kasa tabuka komai da majalisar dinkin duniya ta yi musamman ma kwamitin tsaro game da ci gaba da kisan kare dangi da HKI take ci gaba da yi kan alummar falasdinu. Wannan mayar da martani mai zafi daga hamas yana zuwa ne bayan da fira […]

Habasha za ta ƙaddamar Da Tashar Lantarki Mafi Girma a Afirka

Kasar Habasha za ta kaddamar da wani babban dam da aka gina a kan kogin Nilu bayan shafe shekaru goma sha hudu ana aikin. Babbar madatsar ruwa ta Habasha, wacce za ta kasance tashar samar da wutar lantarki mafi girma a Afirka. Tasha ce da za ta riƙa samar da wuta mai karfin wutar lantarki […]

Iran Da Oman Sun yi Kira Ga Mdd Ta Dakatar Da Kisan Gilla Da Isra’la Ke yi A Gaza

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi da kuma Badar al-busaidi sun tattauna ta wayar tarho kan danagantakar dake tsakanin kasashen biyu kuma sun bukaci majaliasar dinkin duniya da ta dakatar da HKI ci gaba da kisan kare  dangi da take yi a yankin Gaza. Kasashen Iran da Oman suna da tsohuwar danagantaka tsakaninsu kuma […]

Iran za ta wanzar da hadin kai a duniyar Musulmi (Pezeshkian)

Shugaban kasar Iran Massoud Pezeshkian ya tabbatar da cewa Iran ba ta neman fada da wata kasa ta musulmi ba, kuma tana ci gaba da jajircewa wajen ingantawa da kuma wanzar da hadin kai a tsakanin kasashen musulmi. Da yake jawabi a taron kasa da kasa na hadin kan musulmi karo na 39 a birnin […]

Faransa : Majalisa ta yanke kauna ga firaminista Bayrou

Majalisar dokokin Faransa ta kada kuri’ar yankan kauna wadda ta kawo karshen gwamnatin Firaministan kasar Francois Bayrou. Yan majalisar dokokin kasar sun kada kuri’ar yanke masa kauna da kashi biyu cikin uku a jiya Litini. Bayrou dai ya shafe watanni 9 kacal akan wannan kujera a matsayin Firaminista na shida karƙashin shugabancin Emmanuel Macron da […]

Kungiyoyin Falastinawa sun bayyana farmakin Kudus da aikin Jarumtaka

A cikin jawabai daban-daban da kungiyoyin gwagwarmayar Falastinawa sukayi sun yi marhabin da farmakin da wasu mahara suka kai a jiya Litinin a arewacin birnin Quds, inda suka bayyana hakan a matsayin martani ga kisan kiyashin da gwamnatin sahyoniyawa take yi kan al’ummar Falastinu, musamman a zirin Gaza. Kamfanin dillancin labaran Irna, ya nakalto daga […]

An bude taron sauyin yanayi na Afrika karo na biyu

An bude taron sauyin yanayi na Afirka karo na biyu a birnin Addis Ababa, na kasar Habasha mai manufar samar da hanyoyin magance matsalolin yanayi a nahiyar. Wannan taro na tsawon kwana biyu, wanda Majalisar Dinkin Duniya da Tarayyar Afirka da gwamnatin Habasha suka shirya, na samun halartar wakilai 25,000 da kuma shugabannin kasashe 45. […]

Iran : Araghchi da Grossi zasu gana a wannan makon

Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi zai gana da babban daraktan hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa Rafael Grossi a wannan mako domin kammala sabuwar yarjejeniyar hadin gwiwa. Ganawar za ta iya kawo sauyi wajen tattaunawar diflomasiyya kan batun nukiliyar Iran, da kuma da sassauta matsin lambar da kasashen Turai ke yi […]