Ofishin Firayim Ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya sanar a ranar Asabar cewa “Mashigar Rafah a Gaza za ta kasance a rufe har sai abin da hali ya yi a nan gaba.”
Ofishin Netanyahu ya kara da cewa, bude mashigar ya dogara ne bisa ga yadda Hamas ta aiwatar da tsarin yarjjeniyar da aka cimmawa wajen mika gawawwakin Isra’ilawa da ke hannunta.
Wannan bayanin ya zo ne jim kadan bayan da ofishin jakadancin Falasdinu a Masar ya sanar da cewa za a sake bude mashigar Rafah da ke kudancin zirin Gaza a ranar Litinin mai zuwa.
A nata bangaren, kungiyar Hamas ta bayyana a cikin wata sanarwa cewa, matakin da Netanyahu ya dauka yana a matsayin keta sharuddan yarjejeniyar tsagaita bude wuta, da kuma karya alkawuran da ya dauka ga masu shiga tsakani da masu bayar da lamuni ga yarjejeniyar.
Kungiyar ta yi bayanin cewa, ci gaba da rufe mashigar Rafah, da hana fitar da wadanda suka jikkata da marasa lafiya, da hana shigar da kayan aiki na musamman da ake bukata domin neman wadanda suka bace a karkashin baraguzan gine-gine, hakan zai haifar da jinkirin dawo da gawarwakin Isra’lawan.
Kungiyar ta yi kira ga masu shiga tsakani da masu bayar da lamuni ga yarjejeniyar da su dauki matakin gaggawa don matsa lamba a kan Isra’ila domin bude mashigar Rafah cikin gaggawa, tare da tilasta mata yin aiki da dukkanin sharuddan da ke cikin yarjejeniyar.