Isra’ila Na yi Wa Falasdinawan Da Take Tsare Da Su Kisan Gilla Cikin Dabara

Kungiyar kare hakkin fursunoni falasdinawa ta fitar da rahoton cewa isra’ila tana kisan kare dangi a boye ga falasdinawa da take tsare da su inda

Kungiyar kare hakkin fursunoni falasdinawa ta fitar da rahoton cewa isra’ila tana kisan kare dangi a boye ga falasdinawa da take tsare da su inda gommai suka mutu a shekarar 2025 kawai.

A wani rahoton shekara da kungiyar kare hakkin fusunoni falasdinawa ta wallafa, ta bayyana irin yadda falasdinawa da dama suka mutu saboda tsarin da ya sabama dan adamtaka da isra’ila ke amfani da shi,

A shekara ta 2025 falasdinawa 32 da aka tsare sun hada da wani yaro karami da ya mutu a inda ake tsare da shi, wanda yasa adadin wadanda suka rasa rayukansu sun kai 100 daga watan oktoban shekara ta 2023 lokacin da isra’ila ta kadammar da yakin kisan kare dangi a yankin Gaza.

Rahoton ya nuna cewa ya lura har yanzu hukumomin isra’ila na rike da gawarwaki 94 kuma har yanzu akwai gwamman fusrunoni  falasdinawa da ake tsare da su da karfin tsiya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted