Rahotannin daga Gaza na cewa Isra’ila na ci gaba da kai hare-hare a yankin Falasdinawa, a daidai lokacin da wakilan kungiyar da kuma masu shiga tsakani ke tattaunawa a Masar.
Tankunan yaki da jiragen sama da jiragen ruwa na Isra’ila sun yi luguden wuta a wasu sassa na Gaza a ranar Talata.
A cewar tashar Aljazeera, Hamas ta nunar da cewa ci gaba da kai hare-haren bama-bamai da Isra’ila ke yi a zirin Gaza, wani cikas ne ga sako mutanen da aka yi garkuwa da su.
Qatar mai shiga tsakani a yakin Gaza, ta bayyana cewa, kamata ya yi Isra’ila ta dakatar da ayyukan soji a yankin Falasdinun, kamar yadda shugaban Amurka Donald Trump ya tsara, idan dai har ikirarin firaministan Isra’ila game da shirin Trump na gaskiya ne.”
Bayanai sun ce har yanzu gwamnatin Tel Aviv ba ta cimma burinta na kawar da kungiyar Hamas ba da kuma sako ‘yan kasarta da ake garkuwa da su a Gaza, yau shekaru biyu cif da soma farmakin.
Tun daga ranar 7 ga watan Oktoba Isra’ila ta kashe, Falasdinawa 67,160 galibi mata da yara, tare da jikkata wasu 169,679 a cewar ma’aikatar lafiya ta Gaza.
Isra’ila ta toshe duk wasu hanyoyin shigar da kayan agaji a Gaza da ta yi wa kawayen a daidai lokacin ake fama da matsananciyar yunwa a Zirin.